KUNGIYAR TATTARA BAYANAI DA KUNDIN MARASA LAFIYA TA DUNIYA

MANUFAR WANNAN KUNGIYA.

IFHIMA na wakiltar, sanan tana ciyar da kungiyoyin kwararrun masana tattara bayanai marasa lafiya ta Duniya (HIM) gaba.

HANGEN NESAN KUNGIYA.

Ingantacciyar lafiya a Duniya na samuwa ne ta hanyar ingantaccen tattara bayani akan rashin lafiya.

KIMA DA DARAJAR KUNGIYA.

Shugabanci/ Jagoranci:– Wajen samar da nagartaccen kula da bayanan marasa lafiya.
Nagarta:– Kyakkyawan tsari, mutuntawa dan kiyaye dokokin aiki.
Gamsasshen ban girma:– Rungumar kunzumin al’umar Duniya tare da kulawa da dukkan kima da daraja.
Gamayya:– Wannann kungiya tana na haduwa da kuma rike dangantaka.

Kungiyar tattara bayanan marasa lafiya ta tarayyar kasa da kasa me suna IFHIMA wadda aka sani a da aka fi sani da sunan IFHRO na taimakawa kungiyoyi da kwararru akan harkar tattara bayanan marasa lafiya,. An kafa wannan kungiya ta masana tattara bayanai a shekara ta 1968 a matsayin mahada da za ta tattara kungiyoyin tattara bayanan marasa lafiya a kasashen da suka saudaukar wajen karfafa amfani da bayanan marasa lafiya.

Wadannan hukumomi sun fahimci bukatuwar kungiyar Duniya domin samar da wani yanayi na musayar bayanan da suka danganci marasa lafiya, bayanan kula da tattara bayanan marasa lafiya da kuma fusahar bayani ta zamani.

DALILAN SAMAR DA WANNAN KUNGIYA TA IFHIMA.

Makasudin wannan kungiya shine:-
  • Samar da ci gaba da kuma amfanin bayanan rashin lafiya/ kula da bayanan masara lafiya a dukkan Kasashen duniya.
  • Samar da ci gaba da kuma amfani da bayanan lafiya a duniya/ ko kula da bayanan rashin lafiya a duniya bisa ka’idar da aka samar domin musayar bayanai ko kundin bayanan marasa lafiya/ samar da abubuwan ko tsare-tsaewn da ake bukata wajen ilimin da koyarwa kulawa da tattara bayanan marasa lafiya domin samar da damammaki da sadarwa tsakanin ma’aikatan da suke aiki a fannin tattara bayanan marasa lafiya/ ko kula da tattara bayanan marasa lafiya a dg fadin Duniya.
  • Ciyar da fannin gaba wajen amfani da kimiyyar zamani amfani da na’ura komfuta wajen tattara bayanan marasa lafiya (EHR).
An samu nasarar wadannan kudurce kudurce da buruka ta hanyar hadin kai, yanar Gizo-gizo, musayar sakonni/bayanai ilimin sani da gogewa da kuma kayan aiki a tsakanin mambobin wannan Kungiya

An danganta wannan kungiyata IFHIMA da hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a matsayin hukumar da ba ta Gwamnati ba (NGO) sannan ba a samar da ita domin samun riba ba.

Wannan kungiya na aika wakilanta taron Hukumar lafiya ta duniya daga ko’ina a Duniya sannan tana aiki kafada da kafada da ita (WHO) a ayyuka na musamman a wani abu ko a bisa bukatar hukumar lafiya ta duniyaA fannin tsarin tattara kundin bayanin marasa lafiya da tara bayanai.